Farashin sufurin kwale-kwale a Maiduguri ya doshi dubu 100 bayan ambaliya.

Farashin sufurin kwale-kwale a Maiduguri ya doshi dubu 100 bayan ambaliya.

Bayan sauyin yanayin sufuri na bagatatan ko kuma kace rana tsaka ya riski jama’ar da ambaliyar ta shafa.

Mazauna birnin na Maiduguri  sunce suna fuskantar matsananciyar tsada daga masu kwale-kwale daidai lokacin da buƙatarsu ke ƙaruwa a kusan galibin birnin da ambaliya ta mamaye.

A makon da ya gabata da ambaliyar ta afku masu kwale-kwale na yin aikin ceto ba tare da biyan ko sisi ba amma a yanzu lamarin ya sauya, sakamakon ababan hawa basa iya kaiwa wurare da dama a birnin.

Wani mai suna Baba Ali-Maina ɗan shekara 51 dake da yara 4 ya bayyana ƙaduwarsa bayan  ya biya dubu 70 domin a fitar da wasu kayan wuta da kuma na’urar girki ta gas daga gidansa da ruwa ya mamaye.

Ya gwammace biyan wannan kuɗin maimakon barin kayansa saboda gudun kada barayi da suke shiga su sace.

“To kasan halinmu na ƴan Najeriya muna son amfani da halin da wasu ke ciki don ƙuntata musu, wasu daga cikin masu kwale-kwale na tsawwalawa, wasu kuma na rangwantawa a farashi ƙalilan amma magana ta gaskiya har naira dubu 70 wasu na karba” a cewar Ali-Maina

Sai dai wani matuƙin kwale-kwale Muhammad Yusuf ya ce har yanzu yana aiki kyauta amma kuma yaran da suke tayashi aiki ba ƴaƴansa bane don haka yana biyansu.

“Waɗanann da kake gani ba ƴaƴana bane, yara ne da suke aiki da mu domin taimakawa muke. Idan ka bamu Naira dubu 100 yaran za su raba  domin su taimaki iyalansu” a cewar Yusuf

Tuni illolin da ake hasashen fuskanta a duk lokacin da irn wannan ibtila’i ya faru suka fara bayyana a Maiduguri, tsadar kwale-kwalen wani ƙalubale ne da zai sake jefa jama’a cikin tasku, kari kan fargabar cutuka masu yaɗuwa da ta tursasa hukumomi a yankin umartar jama’a da su ƙauracewa amfani da kayan lambu da kayan gwari da suka fito daga sassan da ambaliyar ta shafa.

Domin kallon cikakken bidiyo na wannan rahoto sai ku shiga wannan adireshi: https://youtu.be/OlLCVGyOV4E

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)