Farashin sufuri ya ƙaru da kashi 50 a Najeriya bayan ƙarin kuɗin man fetur

Farashin sufuri ya ƙaru da kashi 50 a Najeriya bayan ƙarin kuɗin man fetur

Sabon farashin da kamfanin NNPCL ya fitar ya nuna yadda za a riƙa sayar da man a farashin naira 855 zuwa 897 daga naira 568 zuwa 617 da ake sayarwa a baya.

Tuni dai ƴan kasuwa suka sanya nasu farashin kan naira 930 zuwa dubu 1 da 200, lamarin da tuni ya sake jefa jama’ar Najeriyar a tsaka mai wuya bayan ƙaruwar farashin kayaki ciki har da sufuri.

Daga ranar Talata da kamfanin na NNPCL ya sanar da ƙarin farashin man kawo yanzu galibin jama’ar ƙasar sun koma tafiyar ƙasa ga hada-hadarsu ta zuwa wurare masu gajeruwar tazara, yayinda sukan rage zango a ƙafa ga tafiye-tafiye masu doguwar tazara sakamakon tsadar ababen hawa.

A wasu sassan na Najeriyar har zuwa yau Alhamis babu man fetur a kusan dukkanin gidajen mai lamarin da ya taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a bisa tituna.

A jihar Lagos ta kudu maso yammacin Najeriyar, farashin sufuri ya ninka da fiye da kashi 5 ko da ya ke anga ninkinsa da kashi ɗaya tal a wasu yankunan yayinda ake fama da karancin ababen hawa a ɓangare guda kusan kowanne gidan mai ke maƙare da layin motoci.

Can a jihar Kano ma, bayanai sun nuna yadda farashin ababen hawa ya hauhawa matuƙa, bugu da ƙari babu wadatattun babura masu kafa 3 a kan tituna saboda ƙaranci da kuma tsadar man da ake fuskanta.

Daga jihar Sokoto bayanai sun nuna yadda tituna suka zama wayam, yayinda galibin jama’a ke gudanar da tafiye-tafiyensu a ƙafa.

Bayanai daga jihar Cross River sun nuna yadda jama’a ke ƙoƙarin gudanar da wani bore bayan da matakin ƙarin farashin man ya sake tsawwala rayuwa.

A jihar Borno kuwa, bayanai daga birnin Maiduguri sun ce hada-hadar jama’a ta taƙaita matuƙa yayinda ake ganin sintirin motocin jami’an gwamnati kaɗai a manyan tituna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)