
Bayanan da ke zuwa daga manyan kasuwanni sun ce nau’in kayan abincin da suka sauka matuƙa sun ƙunshi Shinkafa da wake da kuma man girki sai gero da masara.
Daga kasuwannin arewacin Najeriyar musamman jihar Kano bayanai sun nuna yadda farashin gero da wake suka sauka matuƙa, lamarin da ya sassauta matsin da ake ciki, kodayake akwai fargabar ganin ba’a koma gidan-jiya ba, ganin yadda tarin ƴan kasuwa ke ɓoye kayansu.
Daga yammacin jiya Lahadi ana sayar da wake duk mudu guda a farashin naira dubu 2500 ko 2700 daga farashin kusan dubu 3 zuwa sama da ake sayar da shi a baya.
Bayanai sun ce buhun shinkafa da ake sayarwa a farashin naira dubu 105 zuwa 110 yanzu ya sauka zuwa dubu 90, yayinda farashin man girki ke ci gaba da faɗuwa.
Dai dai lokacin da watan azumin Ramadana ke ci gaba da ƙaratowa, tarin iyalai masu ɗan canji ne ke sayen kayan abinci suna adanawa saboda fargabar yiwuwar farashin ya sake tashi a nan gaba.
Ɗimbin mutane ne ke sayan kayan amfani suna ajje a lokacin kaka a Najeriyar duk shekara wala’alla saboda fatan samun ƙazamar riba musamman a lokacin na azumin watan Ramadana.
Wasu manoma da sashen RFI Hausa ya zanta da su, sun ce kusan duk shekara haka ce ke faruwa, ta yadda ake tsoratasu su fitar da kayansu a irin wannan lokaci cikin araha amma kuma ƴan kasuwa su saya su ɓoye tare da tsawwala kuɗinsa a nan gaba.
A wannan karon dai ƴan Najeriya sun kai ƙololuwa wajen sayen kayan abinci suna ɓoyewa, ta yadda bayanai ke cewa saɓanin yadda aka saba ganin ƴan kasuwa ko ɗaiɗaikun mutane na yi, a bana lamarin ya haɗa har da kamfanoni da bakuna, cike da fatan tsawwala farashin anan gaba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI