Shugaban ƙungiyar a Najeriya Malam Isa Sunusi ne ya bayyana haka a birnin Maiuguri na jihar Borno, a lokacin wani taron manema labarai da suka shirya.
Ya ce a lokuta da dama jami’an sojojin Najeriya na mu’amulantar duk wani da ya fito daga yankin da mayaƙan Boko Haram suke, tamkar mamban ƙungiyar ta masu tada ƙayar baya ne.
Sojojin Najeriya na ɗaukar duk wani wanda ke zaune ko kuma ya fito daga yankunan da Boko Haram su ke da iko da shi a matsayin mambar ƙungiyar.
Malam Isa Sunusi ya ce sun shigar da ƙara gaban Kotun Hukuntan Manyan laifuka ta Duniya da ke Hague, game da zargin cin zarafin ɗan adam da aka yi a shiyar Arewa maso Gabashin Najeriya.
Ya ce idan har aka yi adanci ga rayukan da basu basu kuma gani ba da mayaƙan Boko Haram da kuma sojoji suka salwantar, to ba shakka nan bada jima wa ba za a kawo ƙarshen yaƙin na Boko Haram.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI