
Jami’in ‘yan sandan Faransa a Najeriya Phillipe Crespo ne ya bayar da wannan tabbacin a karshen mako yayin da ya jagoranci tawagarsa mai jami’ai uku wato Phillipe Barrau, Tony Albaladejo da Cedric Hocquette a ziyarar ban girma da suka kai wa Shugaban Hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa mai ritaya a hedikwatar hukumar dake Abuja.
Ziyarar ta biyo bayan kammala horo na musamman ne ga jami’an rundunar hukumar ta NDLEA da ya gudana a makarantar horas da jami’an hukumar da ke garin Jos, babban birnin jihar Filato, wanda shi ne karo na uku na horo irinsa cikin shekaru biyu da suka gabata.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, Mista Crespo ya yaba wa Marwa bisa irin tarbar da aka saba yi wa tawagar Faransa a kodayaushe da kuma niyyarsa ta hada kai da abokan huldar gida da waje a kokarin da yake yi na dakile matsalar shaye-shaye da fatauci da ko kuma safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.
Ya kuma ci gaba da cewa nasarar ayyukan NDLEA ba wai kawai tana taimakawa wajen kare ‘yan Nijeriya da garuruwan Nijeriya ba ne, har ma da al’ummomin da ke kasashen waje, ta hanyar kokarin da hukumar ta yi na dakile ayyukan ta’addanci da ya yi sanadin kame tarin miyagun kwayoyi da ke kan hanyar zuwa Turai da sauran sassan duniya.
Ya ƙara da cewa, saboda haka gwamnatin Faransa ta hannun rundunar ‘yan sandan kasar za ta ci gaba da bayar da goyon baya da hadin gwiwa ga hukumar ta NDLEA. Sannan Ya ba da shawarar cewa ya kamata a samu ƙaƙƙarfar rubutacciyar haɗin gwiwar a cikin yarjejeniyar hukumomin biyu a cikin sabuwar shekara da muke shirin shiga.
A nasa jawabin, kwararre a fannin fasaha dan kasar Faransa, Phillipe Barrau, ya yaba da kwazon jami’an hukumar ta NDLEA da suka gudanar da atisayen na tsawon makonni uku, inda ya kara da cewa dukkan bangarorin biyu na da darussa da yawa da za su koya daga juna.
Kana Ya ƙara yabawa da goyon baya da kuma iyawar Cibiyar Nazarin Hukumar, wanda ya sa shirin ya gudana cikin nasara, wanda kuma zai dore sama da haka.
Da yake nasa jawabin Shugaban hukumar ta NDLEA a Najeriya Birgediya Buba Marwa mai ritaya ya nuna godiyarsa ga gwamnatin Faransa bisa wannan tallafi da hadin gwiwa. Inda yake cewa "Na tuna a cikin shekarar 2022 lokacin da na ziyarci hedkwatar rundunar ta RAID a Faransa bisa gayyata kuma na nemi irin wannan horo, ban taba sanin wani abu ne da zai samu a wannan gaɓa ba, sannan wannan ba dama ce da za’ayi wasa da ita ba. Ba da daɗewa ba bayan wannan ziyarar, an aika da ƙungiyar kwararru don horar da ma'aikatanmu kuma na yi farin ciki cewa wannan shi ne na uku na aka yi irin wannan atisayen, kuma yana matuƙar tasiri ga jami’an hukumar.
Marwa ya ce yaki da masu safarar miyagun kwayoyi na bukatar hadin gwiwar irin wannan a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI