Fannin tsaro ya samu kaso mafi yawa a kasafin 2025 da shugaba Tinubu ya gabatar

Fannin tsaro ya samu kaso mafi yawa a kasafin 2025 da shugaba Tinubu ya gabatar

A jawabin da ya yi a zauren majalisar dokokin domin amincewa da shi, Tinubu ya ce an warewa bangaran tsaro naira tiriliyan 4.91.

Manyan ayyukan da za  a yi a shekara mai zuwa kuwa an ware naira tiriliyan 4.06 sai fannin kiwon lafiya da aka warewa naira tiriliyan 2.4 sai kuma fannin ilmi da aka warewa tiriliyan 3.5.

Tinubu ya ce kasafin zai taimaka wurin rage tsadar rayuwa daga kashi 34.6 zuwa kashi 15 a shekarar 2025, kuma zai sanya farashin dalar Amurka ya sauka daga 1700 zuwa 1500.

A kasafin na 2025 shugaban ya ce ana sa ran haƙo ganga ɗanyan mai miliyan 2.06 a kowacce rana, za kuma a samu raguwar shigo da tataccen man fetur cikin Najeriya tare da samun ƙaruwar fitar da tatacccen man.

A yayin gabatar da kasafin kuɗin Tinubu ya godewa ƴan Najeriya bisa hadin kan da yake samu a sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi cikin watanni 18 da suka gabata.

Ya ƙara da cewa tattalin arziƙin ƙasar na murmurewa kuma gwamnatinsa za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace don ci gaban tattalin arziƙi, kuma gwamnati ba za ta ja da baya ba kan matakan da take ɗauka.

A bangaran samar da abinci shugaban ya ce ba za su yi wasa wurin tabbatar da wadatar da ƙasar da abinci, kuma suna ɗaukar matakan tabbatar da cewa ƴan Najeriya ba sa kwana da yunwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)