Falasdinawa da Isra'ila ta saki sun nuna alamun azabtarwa da yunwa

Falasdinawa da Isra'ila ta saki sun nuna alamun azabtarwa da yunwa

Kungiyar Hamsa ta Palasdinawa ta ce da dama daga cikin waɗanda aka sako mata daga gidajen yarin Isra'ila alamun azabtarwa da yunwa sun bayyana a jikkunansu, a cikin sabon rukunin da aka saki a ranar Asabar.

A wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila, yanzu haka an sako Falasdinawa 183 daga gidajen yari na Isra'ila.

A yayin da Suka fito sanye da suturu masu launin toka da suka nuna alamun sun shafe shekaru a tsare.

Da yawa daga cikinsu sun sauka a galabaice  ba tare da kuzari ba, yayin sai da aka kaisu wani Asibiti da ke Khan Younis, Gaza, kafin su isa ciki jama’a da ‘yan uwaninsu da suka marabcesu sake saduwa da danginsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)