
Tsohon Shugaban na Najeriya ,ya bayyana cewa, da samun sakamakon zaben, sai ya ji zuciyarsa ta kada, kamar yadda duk duniya ta juya masa baya.
Tsohon shugaban kasar ya kuma amince da rawar da marigayi Raymond Dokpesi, shugaban kamfanin Daar Communications ya taka kafin ya mika mulki ga Buhari.
Ya ce, “Ba abu ne mai sauki ka fadi zabe a matsayin shugaban kasa ba. Za ku yi tunanin duk duniya tana gaba da ku. Amma sai Dokpesi ya gayyace ni kafin in mika mulki. Na tuna abin da ya ce da ni lokacin da na fadi zabe.
“Akwai manyan ’yan Najeriya da yawa (dattijon jihohi) da suka yi magana. Bayan na saurari duk zance, ya taya ni murna tare da kwadaitar da ni in duba fiye da zaben. Haka na tuna da wancan zaman.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI