EU da Jamus sun bai wa Najeriya tallafin kusan yuro miliyan 18

EU da Jamus sun bai wa Najeriya tallafin kusan yuro miliyan 18

Shirin zai laƙume kuɗin da ya kusa yuro miliyan 18 inda za a sada mutane 1,500 da lantarki da kuma samarwa da mutane dubu 30 gas na girki.

Har wa yau a kashi na 3 na wannan shirin za a samar da wutar lantarki mai ƙarfin Megawatts 8.

Tallafin na samar da makamashi ga Najeriya an fara ƙaddamar da shi tun a shekarar 2013 wanda kungiyar tarayyar turai EU da tallafin ƙasar Jamus haɗin gwiwa da ma’aikatar lantarki ta Najeiya.

Kungiyar ta tarayyar turai ta amince ta ƙara zuba kuɗi a kashi na 3 na wannan shiri domin taimakawa ci gaban da kuma samar da tsarin lantarki ta sabbin hanyoyin makamashi da kuma tabbatar da jama’a sun amafana da shirin.   

Mataimakin Ambasadan ƙasar Jamus Johannes Lenhre ya tabbatar da shiri ƙasarsa wurin cimma muradan da Najeriya ta snaya a gaba a fannin makamashi.  

Sakataran ma’aikatar lantarki a Najeriya Mahmuda Mamman ya yaba da irin tallafin da Najeriya ke samu daga kungiyar tarayyar turai da Jamus musamman yadda suke ƙoƙarin tabbatar da samun isashshen makamashi a ƙasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)