A cewar jaridar daily trust, ganawar na da nufin ganin an haɗa karfi da karfe domin kawar da gwamnatin APC mai mulki a zabe mai zuwa.
Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da El-Rufai ya musanta ikirarin da wasu ke yi na cewa yana shirin ficewa daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar adawa.
El-Rufai ya musanta batun
Tsohon gwamnan Kaduna a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi ya bukaci ƴan Najeriya da su yi watsi da ikirarin.
Sai dai jiga-jigan jam’iyyar PDP da APC da SDP sun hallara ganawar ta Talata.
Rahotanni na cewa shugabannin jam’iyyun adawa na tuntubar juna a baya-bayan nan, a wani bangare na yunkurin hadaka kafin zaben 2027 domin hana shugaba Bola Ahmed Tinubu tazarce.
Sabuwar Ƙungiyar Matasa
A ƙarshen makon da ya gabata Mallam Shekarau tsohon gwamnan Kano da ke jagorancin wata sabuwar ƙungiyar matasa League of Northern Democrats (NLD), ya bayyana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar siyasa kafin zaɓen 2027.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, jigo a jam’iyyar PDP kuma na hannun daman tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Segun Showunmi, ya ce taron na ƙunshe da dabaru sosai.
Ya ce taron da shugaban jam’iyyar SDP na ƙasa, Shehu Gabam ya kira, ya samu halartar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Manjo Hamza Al-Mustapha, da shi kansa na ciki.
Showunmi ya ce taron na da nufin samar da kawancen adawa mai ƙarfi gabanin zaɓen 2027.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI