EFCC tn gurfanar da Yahaya Bello a gaban kotu a Abuja kan zargin karkata N80bn

Yahaya Bello, wanda ke wasan ɓuya da EFCC tun cikin watan Afrilun wannan shekara 2024, daga ƙarshe ya kai kansa hedikwatar hukumar da ke Abuja a ranar Talata da misalin karfe 12:55 na rana.

EFCC ta ayyana Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo, bayan da ya kasa amsa gayyata da dama da ta yi masa kafin ta gurfanar da shi a gaban kotu ba tare da ya bayyana ba kan badakalar Naira biliyan 80.

Sai dai wasu bayanai daga jami’an hukumar sun bayyana cewa Bello ya shiga hannunsu ne tsabanin rahotanni da ke cewa ya mika kansa ga hukumar EFCC.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)