EFCC ta tabbatar da gurfanar da Farfesa Usman Yusuf a gaban kotu

EFCC ta tabbatar da gurfanar da Farfesa Usman Yusuf a gaban kotu

Hukumar ta EFCC ta gurfanar da Farfesa Usman Yusuf bisa zarginsa da aikata almundahana, sai dai Mai shari'a kotun Chinyere E. Nwecheonwu ta dage zaman kotun zuwa ranar litinin 3 ga watan gobe.

Mai shari’ar ta ɗage sauraren ƙarar domin sake gyara tuhume tuhumen da ake yiwa Farfesa Usman Yusuf.

Lauyan da ya tsayawa Farfesa Yusuf Isah Dokto Haruna ya nemi bada belin sa, amma kotun ta ƙi har sai zuwa ranar litinin da za'a sake gurfanar da shi.

Mai shari'a Nwecheonwu ta bada umarnin ci gaba da tsare Yusuf a ofishin hukumar EFCC.

Farfesa Yusuf ya yi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu da kuma bukatar ganin an yi adalci wajen jagorancin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)