EFCC ta sake gabatar da sabon zargi kan Yahaya Bello na wawure N110bn

EFCC ta sake gabatar da sabon zargi kan Yahaya Bello na wawure N110bn

Laifukan da gwamnatin tarayya ta shigar ta hannun lauyoyin EFCC, Kemi Pinheiro, Rotimi Oyedepo duka manyan Lauyoyin Najeriya da wasu lauyoyi 7, sun ƙara hada Umar Shuaibu Oricha da Abdulsalam Hudu a matsayin wadanda ake zargi tare da Yahaya Bello.

Sabbin tuhume-tuhumen dai na zuwa ne daidai lokacin da tsohon gwamnan ya ki halartan wata babbar kotun tarayya da ke Abuja inda ake tuhumarsa kan sace zunzurutun kudi har N80.2bn lokacin da yake rike da madafun iko a jihar.

A cikin wani sabon al'amarin kuma, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta bayyana cewa ta bankado wani sabon zamba da ake zargin tsohon gwamnan ya kai har N110,446,470,089.00.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)