Hukumar ta EFCC ta karɓe wannan kadarar ce bayan samun umarnin kotu a ranar 2 ga watan nan na Disamba a ƙarkashin hukuncin da mai shari'a Jude Onwuegbuzie ya yanke.
Rukunin gidajen mai ɗauke da adireshin Plot 109 Cadastral Zone, Lokogoma District, Abuja, ya zama mallakin gwamnati kuma EFCC ta ce, karbewar da ta yi na bisa tsarin tabbatar da cewa, gurɓatattun jami'an gwamnati ba su ji daɗin kadarorin da suka wawure ba.
Hukumar EFCC ta ce, yanzu haka an kaddamar da bincike kan jami'in gwamnatin da ya mallaki wannan katafaren rukunin gidaje ta haramtacciyar hanya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI