EFCC ta kama makusanciyar tsohon gwamnan Delta Okowa kan badaƙalar N1.3trn

EFCC ta kama makusanciyar tsohon gwamnan Delta Okowa kan badaƙalar N1.3trn

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kuma yiwa wasu jami’ai tambayoyi da suka hada da tsohon Daraktan kudi da kuma wani babban jami’in fadar gwamnatin jihar ta Delta.

A cewar majiyoyin EFCC, kudaden da ake zargin sun hada wani bangaren da rabon rarar man fetur da ake wararewa jihohi da ake hako mai na kashi 13 cikin 100.

A watan Nuwamba, an tsare tsohon Gwamna Okowa a ofishin EFCC na Fatakwal, bisa zargin yin amfani da ofishin sa wajen karkatar da kudaden jihar don biyan bukatun kansa.

Da yake tabbatar da kamen, mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya ce, an tsare uwargida Enwa ne domin amsa tambayoyi kan binciken da ake yi na karkatar da kudaden jihar a karkashin tsohuwar gwamnatin. An kuma yi wa wasu jami’an gwamnati tambayoyi.”

Misis Enwa, wacce ta kasance mataimakiyar Akanta Janar a lokacin gwamnatin Gwamna Emmanuel Uduaghan, Okowa ya nada ta a matsayin Akanta Janar a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)