EFCC ta kama ƴan damfara 792 a lokaci guda a Lagos

EFCC ta kama ƴan damfara 792 a lokaci guda a Lagos

Darektan Hulɗa da Jama'a na EFCC, Wilson Uwajaren ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudana a babban ofishin hukumar da ke birnin Lagos.

A yayin gabatar da jawabinsa, Mr. Uwajaren ya bayyana cewa, waɗannan mutanen sun shahara wajen damfara ta yanar gizo, inda suke ɓoye kamanninsu tare da gabatar da soyayya ta ƙarya domin yaudarar jama'a a sassan duniya.

EFCC ta cafke ƴan damfarar ne a ranar 10 ga watan nan na Disamba a wani katafaren gida mai hawa bakwai kuma mai lamba 7, a unguwar Jolayemi da ke Victoria Island a birnin Lagos.

EFCC ta ce, ta shafe tsawon watanni tana tattara bayanai kafin kaddamar da samamen.

Daga cikin ƴan ƙasashen ketare da muka kama, har da ƴan China 148 da ƴan Philippines 40 da ƴan Khazakhtan biyu da ɗan Pakistan guda da kuma ɗan Indonesia guda.- Inji Uwajaren.

Kwararrun ƴan damfarar na ɗaukar ƴan Najeriya aiki tare da biyan su albashin sama da naira dubu 200 a kowanne wata domin taya su gudanar da ayyukansu na cutar al'umma daga sassan duniya.

An dai zuba manyan kwamfutoci na alfarma kuma na zamani a cikin wannan katafaren ginin, yayin da aka gano layukan waya sama da 500 a hawa na biyar kaɗai.

Amurkawa da ƴan Canada da Mexico, su ne suka fi faɗawa komar waɗannan kwararrun ƴan damfarar.

Kamfanin ƴan damfarar na bai wa ƴan Najeriyar da ya ɗauka aiki layukan ƙasashen Turai musamman daga Jamus da Italiya don gudanar da aikin damfarar cikin sauki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)