EFCC ta ce har yanzu tana neman Yahaya Bello ruwa a jallo

EFCC ta ce har yanzu tana neman Yahaya Bello ruwa a jallo

Yayin da tsohon gwamnan ta hannun mai magana da yawunsa Ohiare Michael ya ce yau ya kai kansa EFCC tare da rakiyar lauyoyinsa da kuma gwamnan Kogi Usman Ododo, Hukumar EFCC ta fitar da sanarwar watsi da ikrarin da kuma bayyana cewar har yanzu ta na neman shi ruwa a jallo.

Bello ya shaida wa manema labarai cewar bayan ziyarar domin amsa tambayoyi EFCC ta ce masa ya tafi gida ba tare da masa tambayoyi akan zargin karkata kudaden da suka kai naira biliyan 80 ba.

Tsohon gwamnan ya bukaci hukumar yaki da cin hancin ta ci gaba da aiki da dokokin da suka samar da ita tare da mutunta 'yancin jama'ar kasa, ya yin da ya kara da cewar matakan da ya dauka na kin amsa gayyatar hukumar ya yi su ne domin kare hakkokinsa.

Sai dai mai magana da yawun EFCCn Dele Oyewale ya ce babu gaskiya dangane da mika wuyar tsohon gwamnan, kuma har yanzu suna neman sa ruwa a jallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)