
The Guardian, ɗaya daga cikin manyan jaridu a Najeriya da ke bin diddigi dangane da ƙuɗaɗen ake kashewa domin inganta wutar lantarki, ta ruwaito cewa ware waɗannan maƙudan kuɗaɗe, lamari ne da ya fito fili ƙarara da gazawar Sashen Samar da Wutar Lantarkin da kuma kamfanonin da aka bai wa kwangilar raba ta.
Gudunmawar da kwastoma guda ke kashewa kan lantarki
Bayanan da jaridar ta wallafa, sun tabbatar da cewa sakamakon ƙarin farashin wutar lantarki, a yanzu ɗan Najeriya na biyan Naira 50 a matsayin kuɗin gas don samar masa da kilowatt ɗaya, naira 70 da samar da wutar yayin da yake bayar da naira 11 don isar da wutar a gidansa, sai kuma wasu naira 77, wato jimilce naira 208 kan kowane kilowatta ɗaya.
Bashin da aka ciyo don tallafin wuta
Daga lokacin da aka sayar da hannayen jarinsa zuwa yau, sashen wutar lantarki ciyo bashin da ya zarta dala bilyan 5 da milyan 700 daga Bankin Duniya da kuma Bankin Raya Ƙasashen Afirka, sai kuma wasu Naira tiriliyan 2 da bilyan 300 da aka ciyo daga Babban Bankin Ƙasar CBN.
Ƙarancin wutar lantarki lamarin ne da ke ci gaba da shafar kowane ɓangare na rayuwa a Najeriya, yayin da masu ƙididdiga ke cewa daga shekara ta 2013 zuwa yau, an samu durƙushewa da kuma katsewar wuta a duk faɗin ƙasar sau dai-dai har sau 160 a duk fadin Najeriya.
Dukda rashin wuta amma gwamnati na zuba kuɗi
Duk da waɗannan matsaloli, kusan a kowace shekara adadin kuɗin da ake kashewa a matsayin tallafi ga wutar lantarki sai daɗa ƙaruwa yake yi a Najeriya, inda daga shekara ta 2015 aka tallafa masa da Naira bilyan 225, naira bilyan 302 a 2016 kafin ya tashi zuwa naira bilyan 351 a 2017.
Batun tallafin ya ɗauki sabon salo a 2018 inda aka sanar da ware naira bilyan 440 a matsayin tallafi, sai naira bilyan 528 a 2029.
Duk da cewa an rage adadin abin da ake bai wa wannan bangare a daga 2020 zuwa 2022, amma a 2023 gwamnatin ta sanar da wasu maƙudan kuɗaɗe naira bilyan 618, sai naira tiriliyan 2 da bilyan 300 a 2024, yayin da a wannan shekara 2025 aka ƙara ware wasu naira tiriliyan 2 da bilyan 2 duk don inganta samar da wuta a Najeriya.
Yadda aka raba ƙudin tsakanin Kamfanonin Lantarki
Bayanai da jaridar Guardian ta tattaro daga Hukumar Kayyade Farashin Wutar Lantarki a Najeriya NECR ta fitar, na nuni da cewa, Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya samu sama da bilyan 349 a matsayin tallafi, naira bilyan 269 don (EKEDC) da ke Eko a birnin Lagos, sai naira 320 ga (IE) da ke Ikeja Lagos.
Sauran sun haɗa da naira bilyan 178 ga takwaransu (PHED) na Port Hacourt, bilyan 197 don (BEDC) da ke raba wuta a shiyyar Benin, yayin da (EEDC) da ke Enugu ya samu naira bilyan 193.44 a matsayin tallafi.
Sauran kamfanoni da suka hada da (JED) da ke Jos ya samu bilyan 153 (KAEDC) na Kaduna naira bilyan 173, (YEDC) na shiyyar Yola naira bilyan 103, (KEDCO) da ke Kano bilyan 162.96, sai kuma (IBEDC) na Ibadan naira 294.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI