Dole ne Najeriya ta daina karɓar shawara daga IMF - Attahiru Jega

Dole ne Najeriya ta daina karɓar shawara daga IMF - Attahiru Jega

Farfesa Jega ya ce kodayake yana da kyau a rika hulɗa da waɗannan hukumomin, amma dole ne gwamnatin Najeriya ta yi taka-tsan-tsan don gudun jefa ƙasar cikin gagarumar matsala.

Farfesan ya bayyana haka ne a yayin gabatar da maƙala a wani taron shekara-shekara na manyan darektoci da ke gudana a yanzu haka, yayin da a bana taron ke tattaunawa kan batun samar da ingantacciyar gwamnati domin farfaɗo da tattalin arziƙi.

Har ila yau, farfesa Jega ya buƙaci samar da sauyi a fannin zaɓen shugabanni, yana mai cewa, babban ƙalubalen da ke fuskantar Najeriya shi ne cewa, akasarin jagororin ƙasar ba su kintsa karɓar ragamar shugabanci ba.

Jawabin Jega na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ƴan Najeriya ke ci gaba da zargin Bankin Duniya da IMF da hannu wajen jefa ƙasar cikin mawuyacin matsin rayuwa a sanadiyar shawarwarin da suke bai wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Ƴan Najeriyar sun zargin IMF da tilasta wa shugaba Tinubu janye tallafin man fetur da kuma ƙarya darajar kuɗin ƙasar.

Ba mu da hannu a janye tallafin man fetur a Najeriya - IMF

Asusun Bada Lamuni na Duniya IMF ya bayyana cewa, ba shi da hannu a matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na janye tallafin man fetur a ƙasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke zargin IMF da hannu a janye tallafin man fetur ɗin.

A yayin zantawa da manema labarai a wannan Juma'ar a birnin Washington DC na Amurka, Darektan IMF a yankin Afrika, Abebe Selassie ya bayyana matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na janye tallafin man a matsayin batu na cikin gida.

Matakin na cikin gida ne. Ba mu da wani shiri a Najeriya. Rawar da muke takawa ta taƙaita ne kan tattaunawa a kai a kai, kamar yadda muke yi da sauran ƙasashe irinsu Japan ko kuma Birtaniya. Inji Selassie.

Kodayake Selassie ya bayyana cewa, matakin na gwamnatin Najeriya kan janye tallafin man na da nasaba da manufofinta na dogon-zango domin haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasar.

IMF ta ce ta lura da irin ƙuncin rayuwar da ƴan Najeriya suka faɗa sakamakon janye tallafin, tana mai shawartar gwamnatin Tinubu da ta samar da hanyoyin rage wa al'umma raɗaɗi.

Shugaba Tinubu ya janye tallafin ne jim kaɗan da shan rantsuwar kama aiki a watan Mayun bara bayan ya samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.

Jim kaɗan da janye tallafin ne, farashin litar mai da sauraren kayayyaki ya yi tashin goron zabbi a sassan ƙasar.

Har yanzu dai ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan yadda ake sayar da lita mai a kan naira dubu 1,200 duk kuwa da cewa shugaba Tinubu ya karɓi ƙasar ce a lokacin da ake sayar da lita a kan naira 200.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)