Daruruwan 'yan Uganda ne suka karrama 'yar wasa Rebecca Cheptegei a jana'izar da aka yi

Rebecca Cheptegei, 'yan makonni bayan ta halarci gasar Olympics na Paris,'yar tseren gudun fanfalaki mai shekaru 33, ta samu karramawa daga hukumomin kasar ta Uganda da wasu kungiyoyi da dama daga kasashen duniya.

Idan aka yi tuni ,ta rasu ne bayan da abokinta dan kasar Kenya ya kai mata hari,masu bincike na bayyana cewa Dickson Ndiema Marangach, mai shekaru 32, ya shayar da ita man fetur kafin Sai daga baya shi ma ya cinawa kan saw uta,wanda yan kwanaki bayan hakan ,shi ma yam utu bayan da aka isar da shi asibiti.

 Rebecca Cheptegei Rebecca Cheptegei REUTERS - Dylan Martinez

Masu fafutukar kare hakkin bil adama sun yi tir da samun labarin mutuwar wannan mata a kasar,duk da cewa wannan dai ba shine karo na farko da ake fuskantar kisan mata musamman yan wasan a wannan kasa.

A safiyar  yau Asabar, 'yan uwan ​​'yar wasan kasar Uganda, mazauna yankin, da jami'ai gwamnati, sun taru don yi mata bankwana a kauyen Bukwo da danginta ke zaune, mai tazarar kilomita 380 daga arewa maso gabashin Kampala babban birnin Uganda.

Jana'izzar Rebecca Cheptegei a Kenya Jana'izzar Rebecca Cheptegei a Kenya AP - Andrew Kasuku

Sojoji ne ke dauke da akwatin gawar da aka lullube da tutar Uganda, inda suka kai gawar zuwa zauren taron jama’a.

Daga wannan wuri ne aka kai akwatin gawar zuwa wani filin wasa da ke kusa inda daruruwan mutane suka zo domin bankwana.

 A ƙarshe, an binne Rebecca Cheptegei da rana a cikin itatuwan da ke cikin tuddai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)