Darajar rukunin kamfanonin ta ruguzo a duniya, sakamakon tarin bashi

Darajar rukunin kamfanonin ta ruguzo a duniya, sakamakon tarin bashi

Ta cikin wata sanarwa da cibiyar ta Fitch ta fitar, ta ce kamfanin na Ɗangote ya shirya amfani da wani ɓangare na kuɗaɗe hannun jarin da ya sayar don fara rage basussukan da suka yi masa katutu.

Ko a watan Satumbar 2021 sai da kamfanin mai na Najeriya NNPC ya sayi kaso 20 cikin 100 na hannun jarin matatar man ta Dangote don bashi damar ɗage basussukan da suka yi masa yawa da kuma ɗaga darajar kamfanin.

Shima ta cikin wani bayani da yayi a ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata, Aliko Dangote mammallakin matatar man, ya ce a yanzu kamfanin NNPC ne ke da mallakin kaso 7.2 na hannun jarin matatar.

Bayanai sun ce halin da ake ciki matatar man na shirin sayar da ƙarin kaso 12.7 ga masu saye don ƙarfafa darajar sa da kuma  rage yawan bashin da ake binsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)