Sama da dalibai 10 ne suka samu raunuka biyo bayan wannan rikicin wanda ya afku a ranar litinin.
A cewar wani ganau, fadan ya fara ne da misalin karfe 11 na safe lokacin da wasu daliban makarantar sakandaren gwamnati suka yi arangama da wasu daliban dukkansu a unguwar Adeta saboda rashin jituwa da suka samu a baya. Sheidun gani da ido sun bayyana cewa “Fiye da dalibai goma ne suka samu raunuka a rikicin da ya jefa yankin cikin bala’in.
Dalibai a kan hanyar su ta zuwa makaranta © J-B. PellerinBatun ya fara ne kimanin makonni biyu da suka gabata kuma ya kai ga halin da ake ciki yanzu ana zargin harin ramuwar gayya ne.
" Wasu dai sun danganta wannan ci gaban da aka samu da bangaranci da kuma yaki tsakanin daliban. Da aka tuntubi sakataren yada labarai a ma’aikatar ilimi ta jihar, Peter Amogbonjaye, ya shaidawa manema labarai a jiya cewa hukumomi za su dau matakan da suka dace,banda haka wata sanarwa na kan hanya kan batun.
'Yan Sanda a jihar Lagos yayin da suke yi wa masu zanga-zanga rakiya domin tabbatar da tsaro. 1, Agusta, 2024. AP - Sunday AlambaKakakin rundunar ‘yan sandan, Toun Ejire-Adeyemi (DSP), ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa an kama wasu daga cikin wadanda ake zargin ne a rukuninsu a lokacin da ‘yan sanda suka shiga tsakani ba tare da bata lokaci ba yayin da lamarin ya ci tura. Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin fadan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI