Dakarun sojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 148 tare da kama wasu da dama

Dakarun sojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda 148 tare da kama wasu da dama

Dakarun sojin Najerya sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 148 a hare-haren da suka kai a gidajen kallo daban-daban a cikin makon da muke bankwana da shi.

Kazalika, an kama wasu mutane 258 da ake zargi, ciki har da masu jigilar alburusai biyu da aka bayyana sunayensu da Danweri da Abubakar Hamza.

Daraktan yada labarai na rundunar tsaron ƙasar Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Asabar.

A cewarsa, an kama kunshin harsasai biyu ne a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar Bauchi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)