Wannan nasarar ta tabbatar da ci gaban da ake samu akan mayakan kungiyar Boko Haram da kuma na ISWAP da suka yi ƙaurin suna wajen kai munanan hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya tun a shekarar 2009.
Hare-haren na su ya yi sanadin mutuwar dubban mutane da kuma raba wasu da dama da matsugunansu musamman a jihar Borno da ke ƙasar.
A baya bayan nan dai ƴan ta’addan sun zafafa kai hare-hare a jihar Borno tun daga farkon shekarar nan, ciki har da wani hari da suka kai a garin Dumba a ranar Lahadin da ta gabata inda aka kashe manoma aƙalla 40.
A yayin da Kakakin Rundunar Sojin Kasar, Manjo-Janar Edward Buba, ya ce sojojin sun kashe mayaka 24 a farmakin da suka kai a yankunan Damboa, Bama, da Chibok dukkaninsu a jihar Borno a tsakanin 7 zuwa 13 ga watan Janairun da muke ciki.
Sannan a wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce sojojin sun kama wasu mutum 72 da ake zargin ƴan ta’adda ne, tare da kubutar da mutane takwas da aka yi garkuwa da su.
Buba ya ƙara da cewa a dirar mikiyar da aka riƙa yiwa ƴan ta’addan an samu nasarar ƙwato makamai da alburusai da suka haɗa da bindigogi kirar AK-47 da makaman roka da bama-bamai a yayin farmakin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI