Dakarun Najeriya sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a watan Fabrairu

Dakarun Najeriya sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a watan Fabrairu

Daraktan yaɗa labaran ma’aikatar tsaron, Janar Markus Kangye, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Abuja a kan ayyukan da dakarun ƙasar ke gudanarwa a faɗin ƙasar.

Kangye ya kuma bayyana cewa dakarun sun ceto mutane 320 da aka yi garkuwa da su, a yayin da mayaƙan Boko Haram da ISWAP kimanin 152 suka miƙa wuya da su da iyalansu.

Ya ce dakarun sun kuma ƙwato makamai da suka haɗa da bindigogi guda 296 da harsashai da suka kai ddubu 7 da 245.

A cewarsa, daga cikin makaman akwai bindigogi ƙirar AK 47 guda 159, da kuma waɗanda aka ƙera a gida guda 54, sai harsashann NATO guda dubu 1 da 506 da sauran su.

Janar Kangye ya ce rundunar sojin ƙasar ta gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara ta fannin tsaro da sauran hukumomin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)