
Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar, Manjo Janar Markus Kangye, ne ya bayyana haka a Abuja, a yayin da ya ke yi wa manema labarai bitar nasarorin da dakarun ƙasar suka samu.
Kangye yace dakarun sun kuma ƙwace ɗimbim makamai da ababen hawa a daga ƴan ta’addan a samamen da suka yi daga ranar 14 zuwa 21 ga watan Fabrairu.
Ya ce dakarun sun ƙwace bindigogi da suka haɗa da AK47 guda 46, bindigogin da aka ƙera a gida guda 18, sai bindigogin zari-ruga guda 19 da harshasai sama 1,200.
Kakakin ma’aikatar tsaron ya ƙara da cewa ƴan ta’addda 41 sun miƙa wuya ga dakarun rundunar Operation HADIN KAI a yankin arewa maso gabashin ƙasar, kuma daga cikin su akwai manya baligai 41, sai yara 19.
Janar Kangye ya ƙara da cewa dakarun na Najeriya sun kama masu satar mai a yankin Kudu maso Kudancin ƙasar, sun kuma daƙile satar da kiyasta darajarta ta kai naira 587.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI