Dakarun sun kai wannan samamen ne a yankunan Orsu na jihar Imo, Amaruku da Arochukwu a jihar Abia a kudu maso kudancin ƙasar.
Bugu da ƙari, dakarun sun kama wani babban kwamandan IPOB mai suna Emmanuel Onwugu a ƙaramar hukumar Mbanno a jihar Abia.
Rahotanni sun ce sojoji sun yi fata-fata da sansanin mayakan tare da kwato mutane 14 da suke rike da su.
Baya ga haka kuma sojojin sun bankado wani guri na sirri da ake amfani da shi wajen fasa kwaurin danyen mai zuwa wajen kasar.
Ta cikin wata sanarwa da mai rikon mukamin mataimakin Daraktan rundunar ta 82 Laftanar Kanal Jonah Unuakhalu ya fitar, rundunar sojin ta ce an gudanar da wannan samame ne ranar Laraba a jihar Enugu, kuma a yayin arangamar, dakarun ƙasar sun kashe yan ta’adda 24 tare da kame ɗimbim kwamandojin IPOB.
Sanarwar ta kara da cewa sojojin sun sami wannan nasara ne da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addar tserewa ba shiri, sai kuma guda daya da ya gamu da ajalinsa.
Jami’an tsaron sun kuma yi nasarar kwato kayayyaki da suka hadar da Mota kirar Lexus Jeep da bindigu da kuma jigidar alburusai har guda 3
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI