Gamayyar Ƙungiyoyin Farar Hula ta CSO ta bayyana kaɗuwarta da wannan labarin, tana mai nuna fargaba kan lafiyar jama'a bayan tserewar waɗannan dabbobin.
Shugaban Gamayyar Ƙungiyoyin Farar Hular a yankin Tafkin Chadi, Ahmed Shehu ya ce, kawo yanzu babu wanda ke da masaniya kan halin da dabbobin ke ciki bayan sun tsere daga gidan adana namun daji na Shehu Sanda Kyarimi.
Lamarin na da ban-tsoro, ambaliyar ruwan ta mamaye gidan adana namun dajin. Kodayake babu wanda ya san halin da dabbobin ke ciki, amma tabbas za su nemi mafaka, sai dai akwai yiwuwar su cutar da bil'adama.
Sama da fursunoni 200 sun tsere daga gidan yarin Maiduguri
Sama da fursunoni 200 sun tsere daga gidan yarin birnin Maiduguri da ke jihar Bornon Najeriya bayan ambaliyar ruwa ta rusa katangar gidan yarin.
Ɗaya daga cikin jami'an da ke tsaren gidan yarin da ya buƙaci a sakaya sunansa, shi ne ya tabbatar wa da RFI Hausa cewa, fursunonin sun yi amfani da damar ibtila'in ambaliyar wajen tserewa.
Kazalika jami'in ya bayyana cewa, akwai mayaƙan Boko Haram da ake tsare da su a wannan gidan yarin na New Prison, kuma wasu daga cikinsu sun arce.
A ɓangare guda, akwai wasu fursunoni sama da 200 na daban da su kuma aka sauya musu gidan yari kamar yadda jami'in ya yi ƙarin haske.
Ambaliyar ta kuma rusa ɗakunan jami'an da ke tsaren gidan yarin.
Wannan na zuwa ne a yayin da al'ummar jihar Borno ke cikin zullumi biyo bayan ambaliyar ruwan da ta mamaye yankuna da dama a cikin tsakar dare.
Ya zuwa yanzu babu wani bayani a hukumance game da irin mummunar asarar da aka tafka a sakamakon ambaliyar ruwan wadda ta mamaye dubban gidaje da hanyoyi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI