Da Abacha zai kashe Obasanjo ne ba don na sa baki ba – Gowon

Da Abacha zai kashe Obasanjo ne ba don na sa baki ba – Gowon

Gowon ya bayyana haka ne a wajen bikin Kirsimeti Carol and Praise Festival na Interdenominational Unity Christmas Carol wanda gwamnatin jihar Filato ta shirya. Janar Abacha ya kama Obasanjo a shekarar 1995, inda aka same shi da laifin yukunrin juyin mulkin da aka shirya yi na kifar da gwamnatinsa.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayin ziyara aiki a Goma dake gabashin Congo, 15/11/2008 Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayin ziyara aiki a Goma dake gabashin Congo, 15/11/2008 AP - Jerome Delay

Obasanjo, duk da cewa ya yi zargin cewa ba shi da laifi a juyin mulkin, an yanke masa hukuncin kisa. Ya shafe shekaru uku a gidan yari kafin a sake shi a shekarar 1998 bayan rasuwar Janar Abacha a ranar 8 ga watan Yuni na shekarar.

Gwamnan Filato  Caleb Mutfwang Gwamnan Filato Caleb Mutfwang © Punch Nigeria

 Yayin da Gowon ya kasance babban bako na musamman a wajen taron, Obasanjo ma ya halarci wannan taro a matsayin babban bako.

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Gowon na mai cewa “Na rubuta wa Abacha takarda, na roke shi cewa Allah ya sa shi ya zama shugaba mai kyautatawa ba sharri ba. “Na aika matata da wasikar cikin dare zuwa Abacha da ke Abuja; Na roke shi cewa kada irin wannan ta faru. “Na yi farin ciki da cewa jim kadan bayan haka, abubuwa sun canza, kuma ba wai kawai Obasanjo ya bar gidan yari ba, ya zama shugaban mu a 1999.

“Wannan wani abu ne da addu’a da imani kadai ke iya yi; Na yi farin ciki cewa a yau ni da Obasanjo mun zo don murnar hadin kan Filato,” in ji tsohon Shugaban Najeriya Janar Gowon.

Tsohon shugaban kasar ya ce Filato ta sha fama da kalubale iri-iri na tsaro, don haka karon ya samar da hanyar da ta dace da jama’a su rika haduwa. Ya yabawa gwamna Caleb Mutfwang bisa wasu tsare-tsare daban-daban na inganta zaman lafiya a tsakanin jama'a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)