Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wakilinta ya ganewa idonsa cikar asbitin kula da cutuka masu yaɗuwa na jihar Kano da ake kira IDH ko kuma ‘zana’ maƙil da waɗanda suka harbu da cutar.
A cewar Daily Trust wani jami’in asibitin da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar mata da yawaitar mutuwar da ake gani kullu yaumin sanadiyyar cutar a cikin nasibitin na Zana ko kuma IDH.
Bayanai sun ce har zuwa tsakar ranar jiya anga dandazon marasa lafiyar da ke son ganin likita a asibitin na Zana sakamakon alamomin cutar ta mashaƙon diphtheria.
Rahotanni sun ce makwanni biyu kenan a jere ana ganin ƙaruwar masu fama da wannan cuta da kan riƙe maƙogwaro tare da haddasa zazzabi da kuma ƙuraje a baki ko ɗaɗewar harshe da sauyawar kalar ido.
Wasu majiyoyi sun ce rashin kayakin aiki dama ƙwararrun likitocin da ke duba wannan cuta a sassan jihar shi ne ya haddasa cunkoson jama’a a asibitin wanda ke tsakar birnin Kano.
Tuni dai masu ruwa da tsaki suka ɗaura ɗamarar fara aikin wayar da kan jama’a game da alamomin cutar da kuma yadda za a baiwa kai kariya daga harbuwa da ita, lura da kasancewar cutar ta diphtheria a sahun cutukan da wani kan gogawa wani.
Alƙaluma sun nuna cewa wannan cuta ta fi illa ga ƙananan yara ta yadda ta ke farowa kamar mura gabanin tsananta tare da haddasa asarar rayuka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI