
Sanarwar da NCDC ta fitar tun a ƙarshen mako da ke adadin mutanen 80 wani ɓangare ne na mutum 413 da aka gano sun harbu da cutar cikin makon guda a tsakanin jihohin ƙasar 11.
Tun daga farkon watan Janairun shekarar nan ne Najeriya ta sake ganin ɓullar annobar cutar ta Lassa wadda ke ci gaba da laƙume rayukan jama’a a sassan ƙasar.
Duk da cewa alƙaluman waɗanda cutar ke kashe na matsayin kashi 19.4 ne na yawan masu kamuwa da ita, amma NCDC ta koka da yadda jihohi 3 kaɗai ke ɗauke da kashi 73 na masu ɗauke da cutar.
Shugaban hukumar ta NCDC Jide Idris ya ce ya zamewa jama’a wajibi su ɗauka matakan tsafta da kuma rufe abincinsu don kaucewa shigar ɓera wanda shi ne haddasa cutar.
Jide Idris ya ce akwai buƙatar gidaje su toshe dukkanin wasu hanyoyin shigar ɓeraye a ƙoƙarin yaƙi da cutar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI