A wani jawabi da gwamnan jihar Francis Nwifuru ya gabatar jiya Alhamis kan ta’azzarar masu harbuwa da cutar a sassan jihar ta kudancin Najeriya ya ce cikin mutane 48 da suka harbu da cutar a baya-bayan nan an yi nasarar warkar da mutane 25 waɗanda tuni suka kammala jinya tare da komawa gida.
Sai dai gwamnan ya ce cutar ta hallaka mutane 23 a wani yanayi da jihar ta yi fama da cutar tun daga watan Janairun shekarar nan kawo yanzu.
A jumulla gwamnan ya ce akwai mutanen da yawansu ya kai 394 da suka harbu da cutar ta Lassa cikin watanni 12 a sassa jihar ko da ya ke an yi nasarar daƙileta bayan shigowar ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ciki har da ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières ko kuma MSF.
A cewar gwamnan na Ebonyi duk da cewa wajibi ne su ci gaba da jimama asarar rayukan da aka tafka sanadiyyar wannan cuta, amma dole su jinjinawa ƙungiyar ta MSF wadda ta jajirce wajen daƙile yaɗuwar cutar tare da taimakwa wajen warkar da tarin majinyata.
Najeriya ta yi fama da ta’azzarar wannan cuta cikin shekarar da muke ta 2024 inda aka samu alƙaluman mutanen da yawansu ya kai dubu 4 da 726 da suka harbu a sassan ƙasar.
Cutar wadda ɓera ke yaɗawa masana sun yi ittifaƙin cewa ta fi tsananta a yankunan karkara ta yadda ta kashe tarin mutane.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI