Cibiyar EIU ta ce hana Dangote mai zai shafi shirin ceto tattalin arzikin Najeriya

Cibiyar EIU ta ce hana Dangote mai zai shafi shirin ceto tattalin arzikin Najeriya

Cibiyar ta kuma ce matakin zai dada haifar da faduwar darajar naira, inda ta bukaci daukar matakan gaggawa domin ganin an bai wa matatar irin danyan man da take bukata domin gudanar da aiki gadan gadan.

Wannan cibiyar da ake ganin kimar ta a duniya, ta ce matatar Dangote za ta taka gagarumar rawa wajen sauya fasalin harkokin mai da iskar gas a Najeriya da kuma dakile shigar da tacaccen mai cikin Najeriya.

EIU ta bayyana damuwa a kan irin matsalolin da matatar Dangote ke fuskanta a cikin Najeriya wanda ta danganta shi da siyasa, yayin da ta yi nuni da yadda kamfanin ke fitar da sinadarai da dama da take tacewa daga danyan man zuwa kasuwannin duniya cikin su harda man jirgin sama da takin zamani da iskar gas da kuma dizil da manyan motoci da janareta ke amfani da shi.

Matatar Dangote ta gamu da takkadama tsakaninta da kamfanin man NNPC, matakin da ya haifar da cece kuce mai zafi a Najeriya wadda ta kai ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu sanya baki wajen bada umarnin a sayarwa Dangote danyan mai a farashin naira.

Shugaban kamfanin Aliko Dangote ya zargi NNPC da yi masa zagon gaza wajen gudanar da aikin sa lokacin da shugaban wani sashe na kamfanin ya zargi matatar da fitar da mai mara inganci.

Wannan zargi ya haifar da mahawara mai zafi a ciki da wajen Najeriya, inda wasu fitattun mutane cikin su harda shugaban Bankin raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina ya bukaci taka tsan tsan da kuma tabbatar da ganin cewar Najeriya bata yiwa matatar Dangoten illa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)