CBN ya ce bankunan da aka kama da laifi za su fuskanci biyan tarar Naira miliyan 150, ko hukunci mai tsanani ga waɗanda suka maimata tanadin dokar bankin da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi wato BOFIA ta 2020.
A wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 13 ga watan Disamba ta hannun mukaddashin daraktan sashen kula da harkokin kudi, Solaja Olayemi, CBN ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda bankuna ke cuwa-cuwar takardun ƙudin Naira, maimakon bai wa kwastomi a kanta ko tashoshinsu na cire kudi wato ATM, lamarin da ke haifar da karancin kudi a hannun jama’a tare da dora laifi kai tsaye ga gwamnati.
CBN ya ce zai rika bibiyar sirri lokaci-lokaci a dakunan banki da na ATM a fadin kasar don ganin yadda al’umara ke gudana, domin gano inda ake aikata ba daidai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI