CBN ya ware Naira biliyan 50 domin biyan haƙƙoƙin ma'aikatansa 1,000 da zai sallama

CBN ya ware Naira biliyan 50 domin biyan haƙƙoƙin ma'aikatansa 1,000 da zai sallama

Wani bincike da jaridar Dailytrust da ake wallafawa  a ƙasar ta gudanar ya gano cewa, CBN zai aiwatar da wannan mataki ne kafin ƙarewar shekarar 2024.

A wani mataki na tsarin garambawul ga ma’aikatansa, hukumomin CBN, ƙarkashin jagorancin gwamnan bankin, Olayemi Cardoso, sun bayyana ƙudurinsu na rage yawan ma’aikata.

Majiya mai tushe daga hedikwatar CBN ta tabbatar da cewa za’a kashe Naira biliyan 50 domin sallamar ma’aikatan da za’a kora.

Cikin watanni 10 da suka gabata, CBN ya kori ma’aikata da dama, ciki har da daraktoci 17 da suka yi aiki zamanin tsohon gwamnan bankin Godwin Emefeile, kuma har yanzu ba’a maye gurbinsu ba.

Sanarwar da CBN ta fitar makonni uku da suka wuce wanda wakilin Dailytrust ya samu damar gani, ta ce bankin ya bai wa dukkanin ma’aikatansa damar cike takardar bukatar neman ajjiye aiki da wuri, kuma za’a rufe ranar Asabar, 7 ga watan Disambar bana.

Waɗanda wannan sallama ba ta shafa ba sune wanda ba’a tabbatar da su a matsayin ma’aikata ba, ko kuma ba su shekara su na aiki ba, yayin da aka sanya ranar 31 ga watan Disamba a matsayin lokacin da waɗanda abun ya shafa za su ajjiye aiki.

Jami’an waɗanda suka buƙaci a sakaya sunansu, sun bayyana cewa ya zuwa wannan lokaci jami’ai 860 daga fannoni da dama ne su ka cike wannan takardar neman ajjiye aiki.

Hukumomin CBN sun bayyana matakin a matsayin wata dama ga ma’aikata su bar aiki da wuri, a gefe guda kuma hakan zai basu damar sauya wuraren ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)