Wannan mataki na zuwa ne a dai dai lokacin da masu sana’ar da POS suka koka kan yawan harajin gwamnatin ta ƙaƙaba musu a wani yanayi da matsi hade da taɓarbarewar tattalin arziki ke yi wa masu ƙananan sana’i shaƙar mutuwa a Najeriyar.
Wata sanarwa da CBN ta wallafa a shafinta tun a jiya Alhamis ta bayyana cewa masu sana’ar ta POS na da tsawon wata guda na iya gudanar da harkokinsu gabanin samun kamfani mai rijista da za su koma hada-hada a ƙarƙashinsa.
Wasu bayanai sun ce matakin na CBN na da nufin tsaftacewa da kuma inganta harkar ta POS wadda a juye zuwa babbar harkar hada-hadar kudi musamman tsakanin masu karamin karfi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI