Boko Haram ta hallaka manoma 40 yayin wani hari kan gonakinsu a jihar Borno

Boko Haram ta hallaka manoma 40 yayin wani hari kan gonakinsu a jihar Borno

Rahotanni daga jihar ta Borno sun ce mayaƙan sun farwa gonakin jama’a da misalin ƙarfe 3 na yammaci inda suka buɗe musu wuta, duk kuwa da cewa manoma sun bi dukkanin sharuɗɗan da ƴan bindigar suka gindaya gabanin basu damar yin noma.

Wannan dai ba shi karon farko da al’ummar wannan gari ke ganin kisan manomansu daga mayaƙan na Boko Haram ba, sai dai a baya-bayan nan hare-haren na sauya salo tare da tsananta, lamarin da masana ke ganin baya rasa nasaba da dawowar ayyukan ta’addanci a wannan yanki.

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken rahoto kan wannan hari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)