Boko Haram sun kai hari ofishin ƴan sanda a jihar Borno da ke arewacin Najeriya

Boko Haram sun kai hari ofishin ƴan sanda a jihar Borno da ke arewacin Najeriya

Ƴan sandan da aka kashe an bayyana sunansu da Bartholomew Kalawa mai mukamin sifeta da kuma Mustapha Huzaifat mai mukamin kofur.

Mai magana da yawun ƴan sanda na jihar  Borno Kenneth Daso, ya ce an yi bata kashi tsakanin ƴan sanda da ƴan ta’adda bayan sun kai hari da tsakar dare ranar Alhamis da misalin ƙarfe 12:10.

Ƴan ta’addan sun jefa gurneti kan wani tanti dake bayan ofishin ƴan sandan, abin da ya jikkata jami’ai 2.

Tuni babban sifeton ƴan sandan Najeriya Kayode Egbetokun ya bada umarnin gaggauta kamo waɗanda suka kai harin.

Mai magana da yawun ƴan sandan Najeriya Olumuyiwa Adejobi, ya ce babban sufeton ƴan sanda ya umaci mataimakinsa mai kula da shiyya ta 15 Kenechukwu Onwuemelie da ya haɗa tawaga ta musamman domin tabbatar da an kamo waɗanda suka kai harin.

Wannan harin na zuwa kwanaki kaɗan bayan da mayaƙan na Boko Haram suka kai hari wani sansanin soji dake Borno. Harin ya hallaka sojoji 6 inda suka kashe ƴan ta’adda 34.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)