Birtaniya ta yaba wa NDLEA wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi

Birtaniya ta yaba wa NDLEA wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi

Shugabar hukumar dake kula da harkokin kasashen ketare Victoria Pullen ta bayyana haka lokacin da ta ziyarci shugaban NDLEA Janar Muhammadu Buba Marwa a ofishinsa domin rattaba hannu a kan wata sabuwar yarjejeniyar aiki tare tsakanin bangarorin biyu.

Pullen ta jinjinawa Janar Marwa da jami'ansa saboda rawar da suke takawa wajen yaki da safarar miyagun kwayoyin wanda ta ce ya zama matsala ta duniya dake bukatar hadin kai daga kowanne bangare.

Victoria Pullen na rattaba hannu a kan sabuwar yarjejeniyar aiki tare da Janar Buba Marwa na NDLEA Victoria Pullen na rattaba hannu a kan sabuwar yarjejeniyar aiki tare da Janar Buba Marwa na NDLEA © NDLEA

Shugabar ta ce kame kamen kwayoyin da jami'an NDLEA ke yi shaida ce dake tabbatar da nasarar aikin hukumar, ya yin da ta yaba dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu na aiki tare abinda ya kai ga bude cibiyar binciken da Birtaniya ta ginawa NDLEA a Lagos.

Pullen ta ce sun zuba ido su ga irin nasarorin da za'a samu daga jarin da suka saka a Najeriya wajen yaki da safarar miyagun kwayoyin.

Shugaban NDLEA Janar Marwa ya bayyana farin cikin sa da irin taimakon da suke samu daga gwamnatin Birtaniya da suka hada da Cibiyar ta Marine da kuma ginin ofishinsu a tashar jiragen saman Murtala dake Lagos.

Marwa ya ce tun da suka kadadmar da sauye sauye wajen tafiyar da ayyukan NDLEA sun samu taimako sosai daga bangarori da dama abinda ke nuna karbuwar ayyukan da suke yi.

Shugaban ya ce aikin da suke yi na bukatar taimako da goyan baya saboda tasirinsa wajen dakile safarar kwayoyin dake yiwa kasashe da dama illa.

Marwa ya ce a cikin shekaru 3 sun yi kame sama da dubu 52 tare da kwace tan sama da dubu 8 na kwayoyi da kuma nasarar daure akalla mutane sama da dubu 9.

Shugaban ya ce ganin yawan mutanen da ake samu da hannu wajen safarar kwayoyi tsakanin Najeriya da Birtaniya akwai bukatar karin hadin kai da kuma musayar bayanan asiri a tsakanin su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)