Birtaniya ta tallafawa Najeriya da na’urorin ganowa da kuma kwance bama-bamai

Birtaniya ta tallafawa Najeriya da na’urorin ganowa da kuma kwance bama-bamai

A lokacin da ya ke mika kayayyakin da darajarsu ta kai kusan naira miliyan dubu daya, mataimakin kwamandan rundunar sojojin Birtaniya da ke kula shiyar Yammacin Afrika Kanar Martin Leach, ya ce sun yi hakan ne don ingata alakarsu da Najeriya da kuma taimaka mata wajen yaki da ta’addanci a shiyar Arewa maso Gabashin ƙasar.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake yawan samun hare-hare da ke nuni da cewa Boko Haram na ƙoƙarin farfaɗo da ayyukanta a yankin.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken rahoton wakilinmu na Maiduguri Bilyaminu Yusuf.........

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)