Manjo Janar Christopher Musa, ya karasa da cewa hare-haren da sojoji suka yi a baya-bayan nan, wanda ya kawar da wasu kwamandojin Turji da wasu mukarrabansa, ya karya logon shugaban ‘yan ta’addan.
Hakan ne ya tilasta masa sakin da dama daga cikin mutanen da ya yi garkuwa da su, lamarin da ke nuni da shirinsa na ajiye makamai.
Yan ta’adda suna cikin al’umma; mutane sun san su. Don haka, wani lokacin idan sun gan su, kafin ka sami bayanin, kamar sa'o'i biyu ne - mutumin ya motsa. Don haka idan bayanin ya same ka, kafin ka matsa ya bar yankin.” Inji Janar Musa. Ya kara da cewa, “Amma zan iya gaya muku, mun fitar da na biyu a matsayinsa, mun fitar da mafi yawan hakimansa, hasali ma ya tilastawa yanzu ya saki mafi yawan mutanen da ke karkashinsa. Ina gaya muku kwanan nan ya fara cewa ba ya son komai, a shirye yake ya mika wuya.” Duk da cewa Turji ya bayyana aniyar mika wuya, Janar Musa ya jaddada muhimmancin daure masu aikata ta’addanci, musamman wadanda ke da alhakin mutuwar ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI