Rahotanni sun ce tun ƙarfe 6 na safe ake jin aman wuta a garin har zuwa kusan karfe 3 na ranar yau.
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa Jaridar Daily Trust cewar ba su taba ganin irin wannan musayar wutar ba, kuma har zuwa lokacin da yake magana ana ta artbau tsakanin bangarorin biyu.
Ko a ƙarshen mako saida sabon shugaban rundunar sojin ƙasa Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya ziyarci yankin, inda ya tattauna da dakarun dake aikin tabbatar da tsaro a Tangaza da Ilela a kan muhimmancin murkushe duk wani ɗan ta'adda cikin su harda Bello Turji.
Bello Turji riƙaƙƙen ɗan bindiga ne da ya addabi yankunan jihohin Sokoto da Zamfara, kuma gwamnati ta sha alwashin kawar da shi ko kuma kama shi.
Wannan dai shine karon farko da aka ji ɗuriyar Turji tun bayan da aka kashe ubangidansa Halilu sububu da ya gagari yankin.
Wannan artabu na zuwa bayan da jama’a suka kasance cikin halin fargaba sakamakon bullar ƴan ta’adda na Lakurawa a jihohin da ta’addanci yayi ƙamari.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI