An dai samu bullar cutar kwalara ce a jihar Neja abin da ke kara bazuwa, yayin da a cikin mutane 289 da suka harbu da cutar 17 suka mutu, sannan wasu tara ke kwance a asibiti a fadin kananan hukumomi 11.
Kwamishinan lafiya na jihar Bello Tukur ne ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana a gaban majalisar dokokin Neja a daidai lokacin da aka gayyace shi tare da takwaransa na ma’aikatar lafiya a matakin farko domin bayyana irin kokarin da suke yi dangane da katse karuwar cutar kwalarar dake yaduwa a jihar.
Yanzu haka dai hukumomin kiwon lafiyar sun sunkuya a fafutukarsu ta kawo karshen cutar.
Sai a latsa alamar sauti domin sauraron cikakken rahoton:
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI