Bankin Duniya zai zuba Dala miliyan 600 don gina hanyoyi a Najeriya

Bankin Duniya zai zuba Dala miliyan 600 don gina hanyoyi a Najeriya

Ƙaramin ministan noma da samar da abinci na tarayyar Najeriya, Dr Sabi Aliyu Abdullahi ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja babban birnin ƙasar.

Ministan ya ce ci gaban ya zo ne ƙarƙashin shirin inganta yankunan karkara da kasuwancin kayan noma, inda bankin duniya zai bayar da dala miliyan 500, yayin da gwamnatoci a matakin tarayya da jihohi za su fitar da dala miliyan 100.

Dr Abdullahi ya ƙara da cewa shirin da ake aiwatarwa a jihohin ƙasar 19, nada nufin samar da abubuwan more rayuwa a karkara da kashi 70 na jama’ar ƙasar ke rayuwa a yankunan

Shirin zai kuma mayar da hankali wajen inganta fannin cinikayyar kayayyakin noma, samar da abinci, da kuma kawo ci gaban tattalin arziƙi wanda zai ɗaga ma'aunin tattalin arziƙi ƙasar na GDP a lokaci ƙanƙani.

Sai dai rashin kyawun hanyoyin a karkara na ciwa mazauna yankunan tuwo a ƙwarya, saboda takaita musu gudanar da kasuwanci da sauran al’amarun yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)