Bana goyon bayan kayyaɗe farashin kayayyaki - Tinubu

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke hira ta musamman da manema labarai, inda ya ce abar kasuwa ta yi halinta ta yadda hakan zai sanya farashin ya sauka.

Bana goyon bayan ƙayade farashi, ina mai bada hakuri, abin da ya kamata mu yi shi ne mu ci gaba da samar da kayayyakin da ake buƙata a kasuwa.

Game da batun kudirin dokar haraji kuwa, shugaba Tinubu ya ce babu abin da zai sanya gwamnatinsa ta yi watsi da wannan doka.

Sake fasalin dokar haraji yana nan daram, alamar shugaba nagari ita ce ikon yin abin da ya kamata a lokacin da ya kamata a yi.

To sai dai shugaba shugaba Tinubu ya ce samakon yadda wasu gwamnoni da sanatoci ke sukar dokar, ƙofarsa a buɗe ta ke don tattaunawa a kai.

Dokar wacce a yanzu haka ta ke gaban majalisun dokokin ƙasar, ta haifar da cecekuce musamman yadda jagororin yankin Arewacin ƙasar basa goyon bayanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)