Bamu san lokacin da wutar lantarki za ta dawo Arewacin Najeriya ba - TCN

Bamu san lokacin da wutar lantarki za ta dawo Arewacin Najeriya ba - TCN

Babbar jami’ar TCN, Nafisatu Asabe Ali, ta ce kamfanin ya samu takardar gargaɗi daga Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasar Shawara kan Tsaro cewa, akwai haɗarin gaske shiga yankin da aka lalata manyan turakun lantarki uku, saboda matsalar rashin tsaro.

Babbar jami’ar TCN, Nafisatu Asabe Ali ta ce duk da cewa kamfanin ya riga ya tanadi dukkanin kayan aikin gyaran, amma ba zai iya shiga wajen ba, har sai an samu daidaituwar lamuran tsaro a yankin.

Kimanin mako guda ke nan a jere da aka ɗauke wutar bayan lalacewar babban layin lantarkin Shiroro zuwa Manzo, wanda ke samar da wutar ga akasarin yankin Arewacin Najeriya.

TCN ya bayyana cewa matsalar ta jefa jihohin Arewa maso Gabas da arewa maso Yamma da wani yanki na Arewa ta Tsakiya cikin duhu.

Shugabar kamfanin ta TCN Nafisatu ta bayyana cewa ba za a iya cewa ga takamaiman lokacin da za a gyara layin wutar da ya samu matsala ba saboda matsalar tsaro.

Ku latsa alamar sauti don jin rahoton Khamis Saleh.....

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)