Bama tsoron gwamnonin jihohi mutunta su kawai mu ke yi - Sarkin Musulmi

Bama tsoron gwamnonin jihohi mutunta su kawai mu ke yi - Sarkin Musulmi

Mai Alfarma Sarkin Musulmin ya ce tun kafin samun ƴancin kan Najeriya sarakunan ke mulki, kuma kowa ya san sun fi gwamnonin sanin yadda jama'arsu da ƙasar suke.

Wadannan kalamai sun biyo bayan iƙirarin tsohon gwamnan Neja Babangida Aliyu cewar sarakunan na tsoron gwamnonin jihohinsu.

Kafin a samu gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya sun riga sun fara mulki a wuraren da suka zama Najeriya tun daga 1914, kafin samun ƴancin kai a 1960.

Sarkin Musulmin ya ce sarakunan na mutunta gwamnonin ne kawai saboda darajar da kundin tsarin mulki ya ba su, saboda haka basa kalubalantar su idan sun wuce gona da iri.

Gwamnonin jihohin Najeriya sun mayar da sarakunan abin takawa, ganin yadda suke musu hawar ƙawara da kuma tube duk wanda ya kalubalance su saboda ƙarfin mulkin da suke da shi.

Wannan ya sa a baya aka ga yadda gwamnonin jihohin suka tube sarakuna da dama ciki harda Sarkin Musulmi da Sarkin Gwandu da kuma Sarakunan Kano.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)