Bafarawa ya mika naira biliyan guda domin taimakawa marasa karfi a Sokoto

Bafarawa ya mika naira biliyan guda domin taimakawa marasa karfi a Sokoto

Bafarawa ya bayyana matakin a matsayin cike duk wani gibin da ake iya samu lokacin da ya jagorancin jihar a matsayinsa na 'dan Adam dangane da jagorancin jama'a.

Tsohon gwamnan ya ce a matsayinsa na dattijo mai shekaru 70 da baya bukatar rike wanii mukami na jagorancin siyasa, ya zama wajibi ya taimakawa mutanensa dake cikin halin kakanikayi.

Bafarawa ya yi amfani da bikin mika kudaden wajen neman gafara ga jama'ar jihar Sokoto dangane da duk wani kuskure da wani ke ganin ya masa lokacin da ya jagorancin jihar a matsayin gwamna.

Taron wanda ya samu halartar mutane da dama cikin su harda fitattun malaman addinin Islama irin su Farfesa Mansur Ibrahim da shugaban kwamitin zakkah Sheikh Isa Talatan Mafara.

Jihar Sokoto na daya daga cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suke fama da talauci sakamakon illar da 'yan bindiga suka yiwa jama'a na hana su noma da kiwo da kuma sauran sana'oin da suke a wasu kananan hukumomi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)