Shugaban Hukumar , Mista Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin wata ganawa da mambobin kwamitin majalisar wakilai kan yaki da cin hanci da rashawa a hedikwatar hukumar dake Abuja.
Olukoyede ya nuna matukar damuwarsa kan kalubalen da ke ci gaba da addabar fannin tare da tabbatar wa kwamitin cewa hukumar EFCC ta dukufa wajen bankado duk wata badakala da ta shafi ƙudi.
Ya kuma bayyana cewa hukumar EFCC ta bankado wani al’amari mai cike da damuwa: Inda a cikin shekaru 20 da suka gabata, babu wata ma’aikatar, ko hukumar gwamnati da ta aiwatar da kashi 20 cikin 100 na manyan ayyuka da aka zayyana a cikin kasafin kudinsu. Ya bayyana hakan a matsayin wani gagarumin cikas ga ci gaban Najeriya da samar da ababen more rayuwa ga ƴan ƙasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI