Babu hannunmu a tashin farashin mai a Najeriya - Gwamnati

Babu hannunmu a tashin farashin mai a Najeriya - Gwamnati

Ministan Yada Labaran kasar Mohammed Idris ya ce kamfanin man NNPCL ne ya ƙara farashin sakamakon tsadar man a kasuwannin duniya, yayin da ya ƙara da cewar dokar mai ta kasa da ake kira PIA ta bai wa kamfanin damar yin haka ba tare da samun umarni daga gwamnati ba.

Idris ya ce tun a watan Mayun bara gwamnati ta cire tallafin mai, yayin da NNPCL ya ci gaba da biyan banbancin kuɗaɗen da ake samu domin daidaita farashin, kuma yanzu ya ce ba zai iya ci gaba da haka ba.

Kamfanin na NNPLC ya ƙara farashin lita daga naira 897 zuwa naaira 1,030 a babban birnin tarayya Abuja, yayin da ake sayar da litar a kan farashin naira 998 a birnin Lagos.

Martanin yan Najeriya kan ƙarin farashin litar mai da aka wayi gari da shi a ƙasar Gidan mai na NNPC a Najeriya 02:08

Domin nuna wannan labarin, akwai bukatar ka bayar da izinin sanin bayanan masu bibiya da tallace-tallacen kundin adana bayanai na cookies

Amince Zabin son raina Gidan mai na NNPC a Najeriya AP - Sunday Alamba

Farashin ya kai naira 1,070 a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sai kuma yankin kudu maso yammacin ƙasar da ake sayar da litar a kan naira 1,025. Ana sayar da litar a yankin kudu maso gabashin Najeriya a kan naira1,045, kamar yadda farashin yake a kan naira 1,075 a yankin kudu maso kudancin ƙasar.

 

Sabon ƙarin farashin ya sa ƴan Najeriya da dama tayar da jijiyoyin wuya, inda suka buƙaci gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta gaggauta janye matakin ganin halin da ƴan ƙasar ke ciki na tsadar rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)